Ibn Ghazi al-Miknasi
![]() | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Ameknas, 1437 |
ƙasa |
Marinid dynasty (en) ![]() Wattasid dynasty (en) ![]() |
Harshen uwa | Abzinanci |
Mutuwa | 1513 |
Karatu | |
Harsuna |
Larabci Abzinanci |
Malamai |
al-Fajījī (en) ![]() |
Sana'a | |
Sana'a |
linguist (en) ![]() |
Imani | |
Addini | Musulunci |
Abu Abdallah Muhammad b. Ahmad b. Muhammad Ibn Ghazi al-Utmani al-Miknasi ( Larabci: ابن غازي المكناسي (1437 – 1513) ya kasance masani ɗan ƙasar Morocco a fagen tarihi, shari'ar musulunci, ilimin falsafa da larabci da lissafi. An haife shi a Meknes daga dangin Banu Uthman, a cikin ƙabilar Berber kutama,[1] amma ya yi rayuwarsa a Fez. [2] Ibn Ghazi ya rubuta tarihin Meknes mai juzu'i uku da sharhin Ibn al-Banna, Munyat al-hussab. Domin yin bayani kan aikinsa, Ibn Ghazi ya sake rubuta wata risala (kimanin shafuffuka 300) mai suna Bughyat al-tulab fi sharh munyat al-hussab ("Sha'awar ɗalibai don bayani a kan sha'awar lissafi"). Ya haɗa da sassan kan hanyoyin dabarun koyon lissafi da algebraic. Shi ne mawallafin littafin Kulliyat, ɗan gajeren aiki na tambayoyi da hukunce-hukuncen shari'a a mazhabar Malikiyya. [3]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ Lévi-Provençal, Evariste (1922). Les historiens des Chorfa; essai sur la littérature historique et biographique au Maroc du XVIe au XXe siècle. Paris E. Larose. p. 225.
- ↑ Évariste Lévi-Provençal, Les Historiens du Chorfa, Essai sur la littérature historique et biographique au Maroc, du XVIe au XXe siècle, (1922), pp. 224–30
- ↑ E. Levi-Provencal, Chorfa, p. 231
Ƙara karantawa
[gyara sashe | gyara masomin]- Al-Hamza MH, Ibn Ghazi al-Fasi al-Miknasi and his treatise “The purpose of studying in explaining the desire of calculators" . Academic year-long conference IHST Academy of Sciences. M. 2005. pp. 299–301.